Family Radio Hausa  • Tallafi
Yi kiwon tumakina
© 2012 Family Stations Inc. Ana rike da dukan ikon mallaka. An sake gyaran wannan shafi tun:

“Ya ce masa, har fadi na uku, Siman, dan Yohanna, kana sona? Zuciyar Bitrus ta bache saboda fadin nan na uku da ya yi masa, kana sona? Ya ce masa fa, Ubangiji, ka san abu duka: ka sani ina son ka. Yesu ya ce masa, ka yi kiwon ‘yan tumakina.”
Yohanna 21:17
“Sa’annan shi Sarkin za ya ce wa wadannan da ke hannun damansa, ku zo, ku masu albarka na Ubana, ku gaji mulkin da aka shirya dominku tun kafawar duniya: gama ina jin yunwa, kuka ba ni abinci: ina jin kishi, kuka ba ni abin sha; ina bakonchi, kuka shigo da ni; ina huntanci, kuka tufassada ni; ina ciwo, kuka ziyarce ni; ina cikin kurkuku, kuka zo wurina.”
Matta 25:34-36
“Tumakina suna jin muryata, na kuwa san su, suna biyona kuma; ina ba su rai na har abada; ba kuwa za su lalace ba daidai, ba wanda zai kwace su daga cikin hannuna kuma.”
Yohanna 10:27-28
“Ku karamin garke, kada ku ji tsoro; gama ubanku yana jin dadi shi baku mulkin.”
Luka 12:32
“Ubangiji makiyayina ne; ba zan rasa kome ba. Yana sanya ni in kwanta a cikin makiyaya mai-danya; Yana bishe ni a gefen ruwaye na hutawa. Yana wartsakar da raina; Yana bishe ni a cikin hanyoyin adalci, sabili da sunansa.”
Zabura 23:1-3